WA'AZI








MARAYA ABIN TAUSAYI
Allah Madaukikin Sarki Ya ce:- "Hakika wadanda suke cin dukiyar marayu da zalunci, lallai suna cin wuta ne a cikinsu, kuma za su shiga cikin wata wuta mai tsanani [Surar Nisa'i]

An Karbo daga Abu Huraira (R.A) daga Annabi (S.A.W) Ya ce: "Ku nesanci wasu munanan bbubuwa guda bakwai masu halakarwa!" Sai Sahabbai suka ce: "Ya Manzon Allah wadanne ne?" Sai ya ce: " [1]Yin shirka da Allah, [2] da yin sihiri [3] da kashe rai wace Allah ya haramta kashe ta ba tare da wani hakkin ba [4] da cin riba [5] da cin dukiyar maraya [6] da guduwa daga gun yaki [7] da yin yarfe ga mataye katangaggu muminai kamammu." [Bukhari da Muslim]

Don Allah idan ka gama karanta wa ka taimaka ka turawa sauran 'yan uwa don su amfana.

Ya Allah kayi mana tsari daga aikata wadannan Abubuwa guda bakwai Ameen
MU KOMA GA ALLAH
MUNA TUNATAR DA AL'UMMAR MUSULMI CEWA , BAMU DA MFITA SAI MUN KOMA GA KOYARWAR ADDININ MU.
INA NUFIN YIN AIKI DA SHARI'AR MUSULUNCI , QINYIN AIKI DA SHIRYAR DA MUSULUNCI YA KOYAR SHI YA JEFA MU CIKIN WANNAN YANAYIN DA MUKE CIKI.
ALLAH YACE DA MANZONSA:
..ثم جعلناك على شريعة من الامر فاتبعها ولا تتبع اهواء الذين لا يعلمون انهم لم يغني عنك من الله شيءا..
SNNAN MUKA SAYAKA AKAN AL'AMARIN SHARI'A , KABITA KADA KABI SON ZUCIYAR WADANDA BASU SAN KOMAI BA, LALLAI SU BAZA SU WADATAR DA KAI AGUN ALLAH DA KOMAI BA.
KoWANNE MUTUM IDAN ZAIYI MAGANA AKAN ABIN DA YA SHAFI NAJERIA. SAI YACE ZATA TA SAMI MAFITA TA HANYAR WANNAN ,
SIYASAR .
TO KU SANI SIYASAR NAIGERIA BAZA TA WARWARE MATSALAR MU BA .
MUTUQAR MU MUSULMI NE .
BIN DOKOKIN ALLAH KADAI SHINE MAFITA AGUN MU.
DUK 6ARNAR DA TAKE FARUWA A KASARMU SAKAMAKON ABIN DA MUKE AIWATAR WANE.
..ظهر الفساد في البر والبحر بما كسبت ايد النا س ليذيقهم بعض الذي عملوا...
BARNA TA BAYYANA A TUDU DA CIKIN TEKU SABODA ABIN DA MUTANE SUKE AIKATAWA , DON A DANDANA MUSU SASHIN ABI DA SUKA AIKATA ....
SABoDA HAKA IDAN MUNA SON CANJI TO SAI MU MA MUN CANJA DAGA SABO ZUWA TUBA DA AIKIN ALKHAIRI.
ALLAH YANA CEWA :
.. ان الله لا يغير ما بقوم حتى يغيروا ما بانفسهم..
HAQIQA ALLAH BAYA CANJAWA MUTANE HAR SAI SUN CANJAWA KAN SU DA KANSU.
ALLAH KA CANJA MANA DA MAFI ALKAIRI.
AHMAD IBRAHIM ALKANAWY ALJILAWY .
28___10 ______2018.
NASIHA ZUWA GA SHUGABANNI.
KASANI YA KAI SHUGABA , ALLAH S.W.T YA ZABEKA YA BAKA SHUGABANCIN AL'UMMA BA DON KAFISU BA.
===1__IDAN ILIMI NE AKWAI WADANDA SUKA FIKA , HARMA DA MALAMINKA .
AMMA ALLAH YA QADDARA SU ZAUNA AQARQASHINKA.
====2___IDAN KUDI NE BAKAFI DUK WADANDA KAKE MULKA BA ALLAH YA ZABEKA YA BAKA.
====3___IDAN WAYO NE AKWAI WADANDA SUKA FIKA AMMA ALLAH BAI BASU BA ,
DA DOMIN WAYO NE DA KAI BAZA KA SAMU BA.
====4___KASANI BAKA FI KOWA KYAU BA , AKWAI DUBBABNKA DA SUKA FIKA KYAU , AMMA ALLAH BAI BASU BA .
=====5___DA DOMIN DANGANTAKA NE DA KAI BAZA SAMU BA DIMIN AKWAI "YAN DANGI DA SUNFIKA , AMMA ALLAH BAI BASU BA .
===°=°6__ DA DOMIN LAFIYA NE DA BAZA KA ZAMA SHUGA BA BA DOMIN AKWAI WADANDA SUKA FIKA.
TO SABODA HAKA KASANI ALLAH YA BAKA MULKI NE DON YA JARRABAKA YA GANI ZAKA GODEWA KO BAZA KA GODE BA ,
GODIYAR DA ZAKAYI WA ALLAH SHINE KAYI ADALCI A TSAJANIN WADANDA ALLAH YASA SU AQARQASHINKA .
DA ALLAH YA SO SAI KA ZAMA KAI NE MABIYI , BA KAI AKE BI BA .
TO KAJI TSORON ALLAH KAYIWA MUTANE ADALCI
KA SANI AKWAI RANAR DA ZA'A TASHEKA A TAMBAYE KA , AKAN ABIN DA AKA BAKA !!!;
BA MASU CEWA SAI KAYI DOMIN KOWA TAKANSA YAKEYI.
ALLAH KA BAMU SHUGABANNI NA KWARAI MASU AMANA DA ADALCI .
DEMOCRADIYYA
WALLAHI INA MAMAKIN, DUK MUSULMIN DA YAKE GANIN DIMOKARADIYYA /DEMOCRACY/ ZATA WARWARE MASA MATSALARSA , KO TAWARWARE MATSALAR KASAR NAN TA NIGERIA.
BA ABIN DA ZAI WARWAREWA MUSULMI MATSALAR SU , SAI BIN DOKOKIN ALLAH DA DA'A GA MANZONSA , MUTUKAR MU MUSULMI NE .
MU KOMA GA ALLAH SAI MU RABAUTA DUNIYA DA LAHIRA.
ABIN TAKAICI HAR KAGA WASU SUNA ZAGIN MALAMAI NA ALLAH SABODA "YANSIYASA , MASU TENUWA DA ZATA QARE ,
KO DAYA BAMA GOYON BAYAN , KWADAYAYYUN MALAMAI, MASU NEMAN DUNIYA KAWAI SUN MANTA DA BAIWAR DA ALLAH YAYI MUSU .
TO AMMA KO DAYA BAI DACE BA , A RINKA CIN ZARAFIN MASU MUTNCI KO DA BA MALAMAI BANE .
MUJI TSORON ALLAH MUSANI ZA AYI MANA SAKAMAKON AYYUKAN MU.
ALLAH YA SHIRYAR DAMU TAFARKI MADAIDAICI.
AHMAD IBRAHIM ALKANAWY ALJILAWY , ALGAYAWY.
ADDINI BA RA'AYIN WANI BANE !!!
DAYAWAN MUTANE , ZAKAJI IDAN ANKAWO MUSU , AYAR QUR'ANI KO HADISIN ANNABI S.A.W. ABISA FASSARA DA FAHIMTAR SAHABBAI R.A. DA TABI'AI DA SUKA BISU DA KYAUTATAWA.
والذين جاءوا من بعد هم يقولون ربنا اغفر لنا ولاخواننا الذين سبقونا بالايمان ولا تجعل في قلوبنا غلا للذين ءامنوا ربنا انك رعوف رحيم.
WADANDA SUKA ZO BAYANSU /SAHABBAI/ SUNA CEWA YA UBANGIJI KA GAFARTA MANA TARE DA WADAN DA SUKA RIGAYE MU DA IMANI , KUMA KAGA KASA MANA QIYAYYA DA GABA ACIKIN ZUKATAN MU , DANGANE DA WADANDA SUKAYI IMANI , YA UBANGIJI LALLAI KAI MAI TAUSAYINE MAI JIN KAI.
DOMIN TAFARKINSU SHINE , ALLAH YA TABBATAR CEWA YA YARDA DASHI KUMA SHINE , TAFARKIN MUMINAI .
DOMIN SUNE ALLAH YA TABBATAR , DA CEWA SUNE SUKE KAN MUSULUNCI NA HAQIQA,
SA6A MUSU, 6ATA NE.
SAI KAJI SUNCE SU , BAZASU BAR RA'AYINSU BA .
SUNJAHILCI CEWA SHI ADDINI BIYAYYANE GA ALLAH DA MANZONSA BA RA'YIN WANI BA.
يا ايها الذين ءامنوا اطيعوا الله واطيعوا الرسول ولا تبطلوا اعمالكم.
YA KU WADANDA KUKA BADA GASKIYA , KUYI DA'A GA ALLAH DA MANZONSA , KADA KURUSA AYYUKANKU.
DOLE SAI MUTUM YA YAQI SON ZUCIYARSA SANNAN ZAI SAMU ALJANNAH:
واما من خاف مقام ربه ونهى النفس عن الهوى فان الجنة هى الماواه...
DUK WANDA YAJI TSORON TSAYUWA GA UBANGIJINSA YA HANA ZUCIYARSA ABIN DA TAKE SO , TO HAQIQA ALJANNACE MAKOMARSA.
ANNABI S.A.W. YA FADA CIKIN HADISIN MUSLIM :
.....لا يؤمن احدكم حتى تكون هواه تبعا بما جءت به.
DAYAN KU BAZAI BADA GASKIYA BA HAR SAI YA ZAMO SON ZUCIYARSA TANA BIN ABIN DA NAZO DASHI.
KUMA DUK ABIN DA MUTUM YA AIKATA , DAN KANSA.
..... ان احسنتم احسنتم لانفسكم وان اسءتم فلها ....
IDAN KUKA KYAUTATA , KANKU KUKA KYAUTATAWA , IDAN KUKA MUNANA , KANKU KUKA MUNANAWA.
SABODA HAKA INKAYI ADDINI DAN KANKA , BA WAI MALAMINKA ZA'A BAWA LADAN BA , KUMA BAKA CUTAR , DASHI BA ,
KANKA KAYIWA.
ALLAH KASA MUDACE !!!!!
AHMAD IBRAHIM ALKANAWY.
18___10___2018.

HASSADA MUGUWAR CUTA.
Mece Hassada : ita CE son gushewar ni'ima da aka yiwa waninka .
Ko da abin ba sai dawo gareka ba.
Wannan aqidar yahudawa CE bai kamata musulmi suriqayi ba.
....ام يحسدون الناس على ما اتىاهم الله من فضله ...
Shi mai hassada ALamar yana rigima da Allah ne,
Domin :
1__kamar na nuna cewa kyautar Allah yayiwa wannan Bawan , bai cancaci abashi ba
2__kuma gashi ba zai iya hanawa ba dont bashi yayi wannan baiwar ba.
3__sannan maihassada Baya samun kwanciyar hankali
Don' shi burinsa sai Wanda yakeso za a bawa
Shi kuma Allah Ya bawa Wanda yaso.
Allah ka kiya she mu Hassada Ameen.
HUDUBA ANNABI S.A.W
HUDUBAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM WANDA YAYI A KHUDUBAR RANAR TARA GA WATAN ZUL-HIJJAH, SHEKARA TA GOMA DA HIJIRA A DUTSEN ARAFAT (RANAR ARFA KENAN).
ANNABI (SAW)YA FARA DACEWA:
“Ya ku MUTANE ku bani hankalinku, domin mai Yiwuwa bazan sake kasancewa da ku bayan wannan shekaran ba, saboda haka ku saurari abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar da abinda zan gaya maku) ga wadanda basa wannan wuri a yau.
Ya ku mutane kamar yadda kuka riki wannan wata, (NA HAJJI) da wannan rana (TA ARFA) da kuma wannan gari (NA MAKKA ) da GIRMA kuma abin TSAREWA, to haka kuma ku riki Ran MUSULMI da kuma DUKIYOYINSU da girma abin kuma karewa, ku maida wa Mutane kayan da suka baku AMANA. Kar ku CUCI kowa, saboda kar wasu su cuce ku, ku tuna fa, hakika ALLAH zai yi sakayya akan ayukakanku, ALLAH (SWT) ya hana cin riba,(wato KUDIN RUWA) saboda haka, duk abin da aka kulla ta kudin ruwa sai an warware shi.
Ku yi hattara da SHAIDAN, domin kiyaye ADDININKU. Yanzu kan ya fidda ran batar da ku akan manyan abubuwa (na sabo) saboda haka ku guji binshi akan kanana.
Ya ku jamaa hakika kuna da hakki bisa MATAYENKU, amma suma suna da hakki bisa kanku, to hakkin su ne akanku da KUCIYAR dasu, Kuma ku TUFATAR dasu akan jin kai. ku bi dasu kyakkyawan biyarwa, ku kuma tausasa musu domin su majibintan al amurran kune, kuma mataimakan ku, Hakki ne akansu da kar su yi abota da duk wanda ba kwa so, kuma su nisanci ZINA.
Ya ku jama'a kuyi kyakkyawan bauta ga ALLAH (SWT) ku tsaida SALLOLI biyar(5) na farilla, Ku AZUMCI Watan RAMADAN ku Kuma bada ZAKKA. Ku aikata aikin HAJJI in har kun sami daman yi. KU SANI FA, ko wane musulmi dan uwan musulmi ne. Dukkan ku dai dai kuke. Ba wanda yake da fifiko saman wani sai ta tsoron ALLAH, da aikata kyawawan ayyukka.
Ku tuna fa(ya ku jama'a) wata rana za ku tsaya gaban UBANGIJINKU, domin sakamakon ayyukanku, saboda haka ku yi hattara kada ku yi sake da hanya MADAIDAICIYA bayan na kau.
Ya ku jama'a ba wani ANNABI ko MANZO da zai zo bayana kuma babu wani ADDINI da zai zo (bayan addinin MUSULUNCI), saboda haka kuyi tunani sosai akan wannan magana dana gaya maku, kuma ku fahimce ta (sosai).
Zan bar maku abubuwa guda biyu (2); ga (ALKUR'ANI) ga kuma (SUNNAH) ta. In kun bi wannan ba za ku ta ba bata ba. Duk Wanda ya ji wannan sako to ya jiyar da wadansu, suma su jiyar da wasunsu, kuma sau da yawa wadanda za su ji magana daga karshe sufi masu ji na yanzu fahimtar abinda nake fada.
YA ALLAH ka zamo shaida agareni, cewa na isar da aikenka zuwa ga bayinka.”
Yan uwa ku watsa wannan KHUDUBAR ga yan uwa musulmi wanda kamar yau akayi ta!!!
Allah duk wanda ya tura wannan khuduba ya Allah ka sadashi da annabin Muhammad (saw),ya Allah kabiya masa dukkan bukatunsa na alkhairi.
GOMAN FARKO
Falalar Goman Farko Na Zul-Hajji
An karbo Hadisi Daga ibn Abbas (R.A) ya ce
Annabi (SAW) ya ce:
Ranar daya ga watan zilhijja ita ce ranar da Allah
(swt) ya gafartawa Annabi Adam (A.S). Duk
wanda ya azimci wannan rana Allah(SWT) zai
gafarta masa kowane irin zunubi tsakaninsa da
shi.
(2) Ranar biyu ga Zulhijja ita ce ranar da Allah
(SWT) ya karbi Addu’ar Annabi Yunus (A.S) ya
fitar da shi daga cikin kifin da ya hadiye shi.
Wanda ya azimci wannan rana yana da lada
kwatankwacin wanda ya raya shekara da ibada .
(3) Ranar uku ga Zulhijja ita ce ranar da Allah
(SWT) ya karbi addu’ar Annabi Zakariyya (A.S)
ya ba shi haihuwa. Duk wanda ya azimci wannan
rana Allah (SWT) zai karbi adduo’insa.
(4) Ranar hudu ga Zulhijja ita ce ranar da aka
haifi
Annabi Isah (A.S). Duk wanda ya azimci wannan
rana Allah zai kare shi daga talauci da musibu.
(5) Ranar biyar ga Zulhijja ita ce ranar da aka
haifi
Annabi Musa (A.S). Duk Wanda ya azimci
wannan rana Allah (SWT) zai kare shi daga
munafunci ko azabar kabari.
(6) Ranar shida ga Zilhijja ita ce ranar da Allah
(SWT) ya yi budin alkhairi ga Annabi (SAW). Duk
wanda ya azimci wannan rana Allah zai dube shi
da rahama, kuma ba zai azabtar da shi ba.
(7) Ranar bakwai ga Zulhijja ita ce ranar da Allah
(SWT) zai sa a rufe kofofin wuta, ba za a bude su
ba har sai wadannan kwanaki goma sun wuce.
Duk wanda ya azimci wannan rana Allah zai rufe
masa kofofi talatin na tsanani a rayuwarsa a
buda masa kofofi talatin na sauki.
(8) Ranar takwas ga Zilhijja ita ce ranar da ake
cewa, ranar tarayya. Duk wanda ya azimci
wannan ranar, babu wanda ya san adadinsa sai
Allah.
(9) Ranar tara ga watan Zulhijja ita ce ranar
hawan Arfa. Allah yana gafartawa duk Alhazan da
ke wurin Arfa. Wanda kuma ba ya wurin aikin
Hajji, idan ya azimci wannan ranar, Allah yana
gafarta masa zunibinsa na shekarar da ta
gabata,
da kuma shekarar da ke tafe.
(10). Ranar goma ga Zulhijja ita ce ranar layya.
Duk wanda Allah ya horewa abin da zai yi layya,
idan ya yanka dabbarsa, digon jini na farko da zai
fara diga a kasa zai zama gafara gare shi da
iyalinsa. An so wanda zai yi layya da wanda ba
zai yi ba ya kame bakinsa sai bayan an dawo
daga sallar idi, ya ci abinci ko wani abu daga
cikin layyarsa. Allah zai ba shi lada wacce ta fi
Dutsen Uhud girma da nauyi.Kuma ana so ya
raba namansa kashi uku. Kashi na farko sadaka,
kashi na biyu kyauta, kashi na uku kuma domin
iyali.
Allah Ya Bamu Ikon Azumtar Dukkan Wadannan
Ranakun,kuma ya sadamu da falalar da ya
tanadar ga masu Ibada a wadannan ranaku.
DAMA DAMA
DAMA DAMA, CHAKWAKIYA, HANTSALBATSAL, SOKIBURUTSU, HARBATAMATI, KWA6A, TuFKE DA WARWARA, KWASHE KWASHE,
ADDININ "YAN QUR'ANIYYU !!!!!
Suna aiki da hadisi , kuma suna qaryata shi, suna zaginsa ,
Kuma suna kafirta mai aiki da hadisi , kuma suna cewa ai muna karatune da:
#__WARSHU, ____ RIWAYA CE
#___HAFSU, ________RIWAYA CE
Qur'ni ta hanyar riwayar HADISI aka same shi,
1__WARSHU ALMAJIRIN IMAMU NAFI'U ALMADANY,
2__HAFSU ALMAJIRIN IMAMU AASIM ALKUFY.
Qur'ani An same shi ne tahanyar Talaqqy ,
Daga Malaa'ika Jibril A.S. zuwa ga Annabi S.A.W.
Daga Annabi S.A.W. zuwa sahabbai R.A. Zuwa Tabi'ay riwaya har zuwa qarni na 5 biyar bayan Hijra.
To ga tambayoyi:
1__ Kalmar shahada acikin hadisi tazo , kuma da ita ake shiga musulunci , to ta hanyar hadisi ma ake Shiga musulunci. To kawo wannan Kalmar aqur'ani ??
2__mataa nawa musulunci ya yarda a aura a qur'aniyyance. ?
3__Alqur'ani ya fadi a dadin watanni goma sha biyu 12 , Ku kawomin sunayen watannin a qur'ani . ???
Allah ka kiya shemu son zuciya da Jahilci.
AHMAD IBRAHIM Alkanawy Algayawy.
QUR’ANIYYUN
"YAN QUR'ANIYYUN, SUNE " YAN TATSINE, SUNE DIGAWA, "KUNTU HAUTSIN, SUNE FAGWALAWA, SUNE " YANTABARMI,
Da dai sauran sunaye da ake kiransu.
Suna da Aqidu da sukai tarayya akansu , da kuma wadanda suka sa6awa juna.
AQIDUNSU NA TARAYYA :
1___qaryata Hadisain Annabi S.A.W.
2___Kafirta masu aiki da Hadisi.
3___zagin littattafan Fiqhun da malamai suka fitar da ma'nonin qur'ani da hadisi. Da kuka kiran duk wani littafi da sunan littaki , wai da za'a ajiyesu zasu tattakesu da qafa.
4___fassara qur'ani da son zuciya , da qinyarda da abin Annabi S.A.W ya fassara shi acikin hadisi.
5___Rashin iya karatun qur'ani dai dai , saboda adawa da ilimin tajwidy run dai a Hadisai yazo.
6__ Haramta duk abin yazo na rayuwa idan sun kasa gane haqiqaninsa.
Kamar:
#_ Television , Radio, computer
Waya ,
Mota , keke Babur DS.
Amma wannan sun barta domin suka sun da baza su iya ba, saboda zamani , yanzu har waya da sauran ka yayyaki suna amfani da su.
Domin in sunyi tawaye ga wadannan yan mutane baza su bisu ba.
7___shine rigima da musulmi da hukuma .
Ahmad Alkanawy Aljilawy Algayawy.
DAN QUR'ANIYYU !!!
A DAI NA QAZAFI
Naga wani Dan qur'aniyyu, yayi rubutu a wannan saha, yana cewa:
Hadisai su suka kawo rikici da sa6anin da musulunci yake ciki.
To idan mafadin magana wawa ne to majiyinta ba wawa bane.
#__ Anyi rikicin "yan tatsine , a Borno Wanda masu da,awar aiki da qur'ani ban da hadisi ne.
Sannan , anyi irinsa a Gombe da Adamawa,
Haka kano anyi maitatsine.
Duk suna cewa hadisi ba kyau .
Suna cewa littafi , wai sunansa littaki , zasu tattakesu.
To wadannan aiki da hadisi sukai suka tada rikici, ko hadisi ne yasasu.
Ahmad Ibrahim Alkanawy.
IBLISIYYUN
"YAN QUR'ANIYYUN.
Ko
IBLISIYYUN ???
Wannan aqida tacewa da aqur'ni kawai za'ayi aiki , to ta sa6awa shi Kansa qur'anin.
Ga abubuwan da ke nuna jahilcin masu wannan aqida :
1__wacce kalma ake fada ashiga musulunci ?
Dole kace :
اشهد ان لا اله الا الله و اشهد ان محمدا رسول الله.
To INA wannan lafazin yake ackin qur'ani .babu.
# Ashe ana shiga musulunci ne ta hanyar hadisi .
To in bayar da ba , haka shigo ba kenan ,idan musulmi suna magana kar yasa Baki har sai ya shigo.
2__Duk qur'ani ta hanyar riwayar hadisi aka samo shi, wato qur,ani da qira'arsa ta hanyar hadisi yazo.
Shiyasa ake cewa :
Riwayar Warshu ko Riwayar Hafsu. Duk wadannan marawaitane ba sunansu acikin qur'ani amma sai kuce mu warshu mukeyi , to INA lafazin warshu acikin qur'ani ??
#_ warshu dai almajirin Imamu Nafi'ul Madany ne.
#_Hafsu kuma Almajirin lmamu A'sim Alkufy ne.
Da sauran qira'o'in
#__Ibn kathir Almakky
#__Ibn Amr Addamashqy
#_Abu Aamir Albasary
#__Hamza Alkufy
#__Aliyu Alkisa'i Alkufy
Wadannan sune qurra'ussab'a duk qur'ani ta hanyar hadisi aka rawaito shi , idan baka yarda da hadisi ba to ,baka yarda da qur'ani ba.
3__lbadu kamar salla ,
Lafazin sallah yana nufin Addu'a
Kamar acikin suratul Ahzab. :
ان الله و ملاءكته يصلون على النبي يا ايها الذين ءامنوا صلوا عليه وسلموا تسليما،
Haqiqa Allah da mala'ikunsa suna salati ga Annabi ya Ku Wanda kukayi imani kuyi salati da sallama ...
Kuma Allah yace :
...واقيموا الصلاة واتذكاة...
Tambaya: salla Allah da mala'iku za suyiwa Annabi da ruku'u da sjjada, ??
Ko Addu'a.
Yaya Allah da mala'iku sukayi salatin kawo aqur'anin ??
4__Allah yace:
يا ايها الذين ءامنوا اركعوا واسجدوا واعبدوا ربكم وافعلوا الخير لعلكم تفلحون.
..يا مريم اقنتي لربك واسجدي واركعي مع الراكعين.
Kaga qur'ani yace ayi Ruku'u da sujjada , to a ina kuma yace a dago daga ruku'u ko sujjada a duk cikin qur'ani ??
To salla zata yiyu ba wannan .sai ka koma hadisi.
5__shin annabi S.A.W. zuwa yayi ya ajiye qur'ani ya tafi bai wa kowa magana ba, idan yayi magana to me yace kuma a INA zamugani?
Yayi aure , ya aurar ya aura "ya " yansa da matansa kawo su acikin qur'ani tunda baka yarda da hadisi ba,
Shin annabi bai magana ba har ya koma ga Allah ko yayi ? Gashi Allah yace :
وما ينطق عن الهوى ان هو الا وحي يوحى.
Annabi baya magana akan son zuciyar ,face wahayi da aka yi masa.
Shin baiyi magana ba sai qur'ani ??.
6__Ku kawo adadin raka'o'in ko wacce sallah acikin alqur'ani , da yadda ake karatunta ?
Allah ka kiya shemu son zuciya da Jahilci
Jaririn Almajiri .
AHMAD IBRAHIM, Alkanawy Aljilawy Algayawy.
HALAKA
"YAN KOGON HALAKA YAUSHE SAHABBAI SUKA ZAMO MUNAFUKAI DA KUKE FASSARA , CEWA AYOYIN DA AKAYI MAGANA AKAN MUNAFUKAI DA SAHABBAI AKE !!!!!
Ta ya ya sahabi zai zama munafuki ? SAHABBAI da ban munafukai da ban .
Da wannan Luke fakewa kuna zagin SAHABBAI ,
Ina yi muku nasiha da kuji tsoron Allah , kusan za,ayi muku tambayoyi akan abin da Luke fada ,
وان عليكم لحافظين كراما كاتبين يعلمون ما تفعلون
ما يلفظ من قول الا لديه رقيب عتيد،
Lallai at are daku akwai masu kiyaye abin da Luke aikatawa , masu karanci ne , kuma suna rubuta abin da Luke aikatawa.
Ba Wanda zai furucin wata magana face ,akwai makusanci gare shi ,Wanda baya rabuwa da shi, /malaa'ika/.
Saboda haka , Ku gane cewa fatan mu Ku dawo kan haqiqanin koyarwar Qur'anic da hadisan Annabi Ingattattu .ba kwashe kwashen riwayoyi na ma6arnata kuma maqaryata ba .wa danda sukewa bayin Allah qarya , masu msonzuciya iri su:
Abu miknab , Lud bn yahya.
Da Jabir Aljufy
Da irisu. Said bn Abdillah
Ds.
Wadan da malamai sun tabbatar da cewa maqar yata ne
.
Had ya shahar cikin zantukansu suna cewa:
اذا احسنا شيء جعلناه حديث،
Iran mukaso kyautata abu said mumai dashi hadisi .
Su qirqiri hadisin qarya kawai suce annabi .s.aw. Yace saboda sunan abin yazamo kar6a66e agun jama,a.
Allah kiya shemu bin son zuciya .
.
Allah , ya kiya shemu son zuciya .
MATA
MASU DA'AWAR KARE HAQQIN MATA
KO MASU 6ATA MATA ??
Kamar yadda mukayi bayani a rubutun my na baya , irin yadda sauran addinai da al'adu suka wulaqantar da mata, wajen nuna cewa su haja CE ko wahala ce arayuwar mai mallakarta .
Kuma kaya be na gado , agun duk Wanda ya mallake su.
Sai da musulunci yazo sannan , ya basu "yanci.
Kuma ya qwato musu haqqoqinsu .
Musulunci shi ya kawo dai daito tsakanin mata da mata ba tare da zaluntar wani ba.
Farko dai musani Allah shi ya halicci Iowa da komai , saboda haka sai yasamar da abin da zai jagoranci rayuwarsa ,
Ya aiko manzo ya bashi / manual / da zai yiwa mutum da Aljani jagora .
Wannan manual din shine Qur'an da Hadisi .kuma annabin da Allah ya aiko Yafi kowa basira kuma , ya aiko shi ne har atashi duniya duk wani cigaba da zaizo da wata wayewa , Allah yafi kowa saninta , saboda haka wannan sharia tayi dai dai da kowanne zamani.
Duk wani Abu da Dan Adam zai iya shi Allah yake Dora mASA baya doramasa abin da ba zai iya ba,
Ballantana asami wani Dan kanzagi da zai zarqi shari'ar musulunci da gazawa.
Kowa ya fara sanin kan sa da abin da take wajibinsa , da matsayin sa , kada yajefa kansa garin shishshigi cikin halaka.
Musulunci ya bawa kowa aikinsa ,kuma bai yi hakan ba said da ya tabbatar zai iya. Duk Wanda aka zuga shi ya Shiga inda ba NASA ba to yasani ba zai sami nasara ba.
Allah ya haicci maza ya ware musu aiki .misali::
MAZA: su za suyi ayyuka na qarfi da wahala.
Noma , kiwo ,farauta .
Da Acha6a, faskare , Turin kura , da sauransu.
Irin ayyukan da suka shafi harkokin wake .
Sannan su kuma mata ayyukan su daban irin Wadanda suka shafi harkokin gida , kamar .
Girki , shara , rainon yara da sauransu.
Duk kowa Allah ya Dora masa Abun dai dai da yanayin jikinsa.
Yanzu idan akace tayi acha6a kuma dolenta ne, sannan Rana da ciki wata Tara , son Allah zata iya ?? Kuma akwai tausayawa aciki ??.
Ko abawa qaton namiji rainon jariri , shi yana ji da qarfi shi kuma jariri yana ji da rauni, son Allah akwai hikima ?
Saboda haka ke mace zagi be agun ki ace kinyi kama da namiji. Ace jikin ki yamurde da kwanji Lamar namiji , to wanne namiji ne zai sha'awarki , kinzama shi.
To kinsan kanji da abin da ya dace da me , kada akai ki a baro.
Kuma anyi irin wannan awasu qasashe yan suna nan suna da nasani. Lamar yadda ya faru a masar. Aka zuga mata da sunan "yanci suka fito suka qi zaman aure wai suna da freedom ,
Suka tsufa ba miji ba da , kuma ba mai kula da su, a yau dinnan da nasani sukeyi , kukuma sai yanzu za a kawo muku.
LAYYA A MUSULUNCI
LAYYA A MUSULUNCI,
MENE LAYYA :
1_____ MA'ANAR LAYYA :
وهي ما يذكى تقربا الى الله تعالى في ايام النحر بشراءط مخصوصة.
LAYYA ITACE A BIN DA AKE YANKAWA , DON NEMAN KUSANCIN ALLAH MADAUKAKIN SARKI , ACIKIN RANEKUN YANKA /NA SALLAH BABBA/ DA SHARADAI KE6ANTATTU.
2_____ SHAR'ANTUWAR LAYYA YA TABBATA ,
#______ A QUR'AN
....فصل لربك وانحر.
Kai salla do ubangijinka. Kuma kayi yanka,
Malaman tafsiri suka LAYYA ake nufi.
BAYAN KAMMALA SALLAR IDI.
#____ HADISI :
DAGA ANAS DAN MALIK R.A. YACE :
ANNABI S.A.W. YAYI LAYYA , DA RAGUNA GUDA BIYU MANYA MANYA , MASU KAHONHUNA , YA YANKA DA HANNUNSA , YACE BISMILLAHI ALLAHU AKBAR, YA TAKE SHI DA KAFAFUNSA .
DUBA
BUKHARI.Hadisi 5558 DA MUSLIM 1966.
#___IJMA'I:
MALAMAI SUNYI IJMA'I AKAN SHAR'ANTUWAR LAYYA.
DUBA : المغني
Mujalladi 9. SHAFI 345.DAALHAWY NA MAAWARDY.MUJALLADI 19 SHAFI 83
DA المحلى
Mujalladi NA 7.SHAFI 355.
#___ HUKUNCIN LAYYA :
WASU DAGA CIKIN MALAMAI SUNCE WAJIBI CE, GA DUK WANDA ALLAH YA HOREWA.
WASU MALAMAN SUKACE SUNNAH CE MAI QARFI WANNAN SHI RA'AYIN JAMHUR.
#___ DAME AKEYIN LAYYA ??!
LAYYA BATA HALATTA SAI DA DABBOBIN NI'IMA.
SUNE :
1__RAQUMA.
2__SHANU
3__TUMAKI DA AWAKI
BAYA HALATTA DA WASUNSU.
SABO DA FADIN ALLAH:
ليذكروا اسم الله على ما رزقهم الله من بهيمة الانعام...
Don su ambaci sunan Allah abisa abin da Allah ya azurtasu da su daga dabbobin Ni'iMA
SHEKARUN DABBOBIN DA AKE SO A YANKA:
1__RAQUMI : WANDA YA KAMMALA SHEKARU 4 YA SHIGA TA 5 KO TA 6.
2__SANIYA KO SA :
WANDA YA KAMMALA SHEKARA 2 YA SHIGA TA 3
3___ TUMAKI KO AWAKI : WANDA YA KAMMALA 1 YA SHIGA TA 2.
#_____ ILLAR DA TAKE HANA YIN LAYYA DA DABBA:
GUDA HUDU CE. 4
1_ DABBA MAI IDO DAYA KO MAKAUNIYA
2_ DABBA MARA LAFIYA .
3__DABBA GURGUWA.
4__DABBAR DA TA TSUFA TUKUF BA MAI BA DARGO.
IDAN TA BAYYANA DABBA TANA DA DAYA DAG WADANNAN BAYA HALATTA AYI LAYYA DA ITA.
BARRA'U BN AAZIB R.A YACE :
ANNABI S.A.W. YACE :
اربعة لا يجزين في الاضاحي العوراء البين عورها والمريضة البين مرضها والعرجاءالبين ظلعها والكسيرة التي لاتنقي.
DUBA : sunan NA lmamun Nasaa'i
Mujalladi NA 7 SHAFI. 215.
Ibn maajah hadisi NA 3144
Ahmad mujalladi 4
SHAFI. 284.
#___ANA SO WANDA ZAI YI LAYYA , KADA YA ASKE KOWANNE IRIN GASHI A JIKINSA KO FARCENSA ,
YAYIN DA WATAN YAKAMA TUN DAGA DAYA GAWATAN ZULHAJJ HAR SAI YA YANKA DABBARSA.
....قال صلى الله عليه وسلم.اذادخلت العشر واراد احدكم ان يضحي فلا يمس من شعره وبشره شيءا.
ANA SO AYANKA DABBA DA ZARAR AN IDAR DA SALLAH.
SANNAN ANSO AKASA NAMAN UKU
@YI KYAUTA
@YI SADAQA
@CI DA IYALI
ALLAH KA KAR6I IBADUN MU. DA SAURAN AYYUKAN MU .
AMIN
و بالله التوفيق.
AHMAD IBRAHIM ALKANAWY ALJILAWY ALGAYAWY.

No comments:

Post a Comment