إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات
أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ
الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu
Alaikum
Alhamdulillahi Ina kara godewa Allah mai kowa mai komai, yau
burina ya cika na bude website karo na uku wanda nadade ina burin budewa amma
sai yanzu Allah yanufeni da kirkirar wannan shafi mai Albarka.
Na kirkiri wannan
website ne ba don komai ba sai don karuwar musulunci da kuma yadda abubuwa
yanzu suka canja kasancewar komai yakoma sai a internet wato yanar gizo-gizo.
Wannan zai bawa mai karatu damar shiga domin karanta muhimman abubuwa da kuma
dauko karatuttuka daban-daban.
ayau ranar
03/08/2018 na bude wannan shafi
Sannan wannan website
zamu dinga samun update na posting 50% daga wata baiwar Allah mai suna Aisha Abdullahi, 50% Daga Mal. Ahmad Ibrahim Gaya
Wannan Website an
rabashi zuwa categories ko kuma nace label, kokuma nayi muku gwari-gwari
(folder)wanda idan kaduba zakaga ya rarrabu.
Sannan zanyi godiya ga
yan uwa musulmi wadanda suka bada gudummuwa ta bangare daban-daban kamar
wadanda suka dauki nauyi shirya rubutun da za’a dinga uploading, bada shawara,
karfafa gwiwa, gyara yayin da akayi bata.
Irinsu:-
Abdul-aziz Ahmad, Maryam Ahmad, Zainab Muhammad, Umar Bello Sunusi Gaya, Adamu Umar Maitama,
Abdulrashid Abdulmumini Muhammad, Umar Auwalu, Ibrahim Mustapha, Umar Ashir
Bala, Rufa’I Mustapha,Sadiya Muhammad, Aminu Malam, Muhammad Hamza, Muhammad Hassan, Yusif Umar, Abdulkadir Ali Amin, Mal. Ahmad Ibrahim Gaya da kuma Aisha Abdullahi.
Daga Adam M. Adam.
No comments:
Post a Comment